Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar kasuwar abinci ta duniya dake Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa, ta nesanta kanta da wani rahoto da aka yadawa cewa an kama wani dan kasuwar da buhunhunan fulawa gurbatattu sama da Dari hudu.
Sakataren kungiyar kasuwar Kwamaret Rabi’u Abubakar Tinfoil ne, ya bayyana haka ga manema labarai a nan jihar Kano.
Yace mutumin da aka kama kayan nasa ba dan kasuwar su bane, wani dankasuwar ne ya baiwa dan kasuwar Singan aron gurin ajiyar kayan wato store domin ajiye kayansa .
2023: Kwankwaso ya zabi Fasto Idahosa a matsayin mataimakinsa
” Bayan bashi Aron store ne ashe hukumar kare hakkin mai siye da siyarwa ta kano ta samu rahoton gurbatacciyar fulawar har suka zo kasuwar suka kama kayan”. inji Rabi’u Tumfafi
Yace shugaban kasuwar ta Dawanau Alh muttaka Isah ya kirawo Shugaban kungiyar kasuwar Singa domin sanar da shi halin da ake ciki, kuma ya tabbatar da cewa kayan na Dan kasuwar ne ta singa.
Tumfafi yace ita kanta hukumar data kama fulawar ta tabbatar da kasuwar Dawanau ba’a sayar da fulawa, sai dai kaya dangin hatsi, amma fulawa sai dai a kasuwar Singa.
“kasuwar Dawanau bama sayar da kayan da suka lalace, saboda mu kasuwarmu ta duniya ce Muna kiyaye duk wani abu da Muka San ya sabawa doka kuma zai cutar da al’umma”.
Haka zalika yace kungiyar kasuwar Dawanau ba za ta lamunci wani dan kasuwar ko bako ya shigo mata da kayayyaki da basu da inganci ba, ko kuma kaya gurbatattu domin yin kasuwanci ba, inda yace suna ladabtar da duk wanda samu da yin hakan, ya kuma yi fatan al’ummar jihar kano dana kasa baki daya zasu fahimci duk abun da suma fada don gudun fata musu suna.