Daga Safiyanu Dantala jobawa
Wakilin Atiku Abubakar a kano Wanda kuma tsohon dan Majalisar dokokin jihar Kano ne ya Abdullahi Maikano ciromawa ya rabawa mata sama fa dubu daya tallafin na naira dubu hamsin-hamsin a karamar hukumar garun Malam ta jihar Kano domin su dogara da kawunansu.
Alhaji Abdullahi Maikano Chiromawa (Jarman Garun malam) Wanda kuma shi ne jagoran jam’iyyar PDP na karamar hukumar Garun malam yace Wannan shi ne karo na uku da mata zaurawa da marayu ke amfana da tallafin wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar a jihar kano.
Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso
yace an zabo wadanda suka amfana da tallafin ne daga kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano domin su Kara jari a kokarinsa na yakar talauci a Cikin al’umma.
“Dan takarar shugaba kasa a shekara ta 2023 a jam’iyyar PDP daga irin wannan abun alkhairi da aka baku, nasan Kun fahimci Atiku Abubakar zai taimaki al’ummar kasar nan, idan aka zabe shi a zaben 2023, tunda dama ya dade yana taimakawa mata da matasa tun kafin ya zama shugaban kasa”. Inji Maikano ciromawa
Ya bukaci al’umma su zabi Alhaji Atiku Abukar a jam’iyar PDP don kawo sauyi da cigaban tattalin arziki da kuma samar da zaman lafiya a kasar Nigeria, sannan ya bukaci matasa da mata da su yi kokarin yin rijistar zabe don samun nasara zaben Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa.
Alhaji Abdullahi Maikano ciromawa shi ne ya jagoranci mika tallafin kudi na naira dubu hamsin-hamsin ga matan da aka zabo daga kananan hukumomi 44 na fadin jihar Kano.
Tun da fari, shugabar matan tafiyar Atiku Abubakar ta kano, Hajiya Usaina ta yi kira ga mata da su tabbatar a zaben 2023 sun zabi Alhaji Atiku a jam’iyar PDP don magance dumbin matsalolin da suka yiwa kasar nan katutu.
Ta kuma yabawa Jarman na Garun malam kuma wakilin Atiku Abubakar a jihar Kano a bisa namijin kokarin ya ke yi na sauke alkarin Atiku Abubakar a jihar kano. Sannan ta gode wa matan jihar kano dangane da irin hadin kan da su ke baiws tafiyar Atiku Abubakar.
Daya daga cikin wadan da su ka karbi tallafin, Hajiya Zainab Umar Sani (Auty Zee) ta ce tallafin da aka bata zai taimaka wajen ingata rayuwar ta data ‘yan uwanta ko baki daya, ta kuma yabawa Alhaji Abdullahi Maikano Chiromawa jagoran PDP bisa tallafin da suka Sami, tare da bada tabbacin mara baya ga tafiyar Atiku Abubakar.