Babban Sufeton ‘Yan-sandan Najeriya ya haramta amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin hana amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro wadda ake wa lakabi da SPY, a duk fadin kasar.

Umarnin ya biyo bayan irin matakan da shugaban ‘yan-sandan ke dauka na inganta tsaro da dakatar da yadda daidaikun mutane ke fakewa da wannan lambar mota su rika keta dokokin amfani da titi da sauran ka’idoji, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ta bayyana.
Sanarwar ta ce daga yanzu an haramta wa duk wata mota amfani da irin wannan lamba a ko’ina a fadin Najeriya.
Tare da umartar kwamishinonin ‘yan-sanda na jihohin kasar 36 da Abuja, da mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda da su tabbatar da bin umarnin.
Shugaban ‘yan-sandan ya kuma umarci duk ‘yan-sanda da sauran jami’an tsaro da ke aiki da manyan mutane masu amfani da motocin da ke da irin wannan lamba, su tabbatar da bin umarnin ko kuma su fuskanci hadarin kamasu kan kin bin umarnin.
Dokar ta bukaci a kwace dukkanin irin wannan lamba a ko’ina a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...