Gwamnati ta kwace fulawa buhu 487 a kasuwar Dawanau da ke kano

Date:

Hukumar kare hakkin masu sayayya ta jihar Kano ta kwace kimanin buhun fulawa 487, da ta lalace a wajen ajiyar kaya a kasuwar Dawanau da ke birnin Kano.

Jaridar Punch a Najeriya ta ambato jami’in hulda da jama’a na hukumar Musbahu Yakasai a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, na cewa Daraktan riko na hukuma Dakta Baffa Dan’Agundi ne ya bayyana haka a ofishinsa bayan kwato fulawar.

Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso

Dakta Baffa Dan’Agundi ya ce wasu mutanen kirki ne suka bai wa hukumar tasu bayanan sirri game da fulawar wacce aka kawo kasuwar da nufin sayar da ita. Ya kara da cewa gwajin da aka yi wa samfurin fulawar ya nuna cewa tuni ta dade da lalacewa.

Na kagu na sauka saboda mulki akwai wuya – Shugaba Buhari

Haka kuma ya ce hukumar tasu ta kama lemuka masu yawan gaske da suka lalace kuma ake sayar da su a kasuwar Sabon Gari da ke jihar. Gwamnatin jihar Kano ta kwace buhun ‘lalatacciyar’ fulawa 487

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...