Daga Ibrahim Sani Gama
Shugabancin kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa ta sha alwashin bijiro da managartan tsare_tsare domin ganin an bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa, Alh.Mustafa Ali ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake mika sakon kungiyar na barka da sallah ga al’ummar musulmi baki daya.
Alhaji Mustafa Ali yace,yana mika sakon barka da sallah a madadin kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa ga dukkanin al’ummar jihar Kano dana kasa baki daya, ya yi kira ga yan kungiyar da suke gudanar da kasuwanci a jihohin kasar nan talatin da shida da su ci gaba da zama da juna lafiya, musamman da sauran al’ummar da suka samu a yankunan da suke gudanar da kasuwanci nasu .
Hawan Nasarawa:Ganduje ya bayyana dalilin da yasa bai tarbi Sarkin Kano a gidan gwamnatin ba
Ya bukaci al’ummar Najeriya a koina da su taimakawa kasar nan da addu’o’in samun zaman lafiya, duba da halin da al’umma suka samu Kansu a ciki na tabarbarewar harkokin tsaro
“babu Shakka zaman lafiya yana kara bunkasar al’amuran Yau da kullum da samun shugabannin da za su tallafawa harkokin kasuwanci da ma taimakawa al’umma wajen ganin an samu saukin rayuwa”. inji Mustapha
Mustafa Ali yace kungiyar masu fataucin Shanu da dabbobi ta kasa a shiye take wajen hada kai da Gwamnatoci a mata kai daban-daban domin ganin an kare hakkokin yan kungiyar a kodayaushe. Yace kungiyar tana bukatar gwamnati ta tuna da ita, sakamakon gudunmawar da take baiwa duk Gwamnatin da ta zo tun daga jihohi har matakin tarayya, amma ba sa samun wani tallafi daga gwamnatocin.
Daga karshe kungiyar ta godewa ‘yan’yanta bisa cikakken hadin kai da suke bayarwa a duk lokacin da ta bijiro da managartan tsare-tsare domin ganin an kara bunkasa harkokin kasuwancinsu da yadda suke kokarin zama da al’umma lafiya a ko’ina suka samu Kansu a fadin kasar nan.