Kasuwar Dawanau ta taya al’ummar Musulmi Murnar Sallah Babba, tare da bukatar al’umma su yi addu’ar zaman lafiya

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi

 

Kungiyar kasuwar Abinci ta duniya dake kasuwar Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa tana mika sakonta na barka da sallah ga al’ummar musulmin kasar nan.

 

Zababben Sakataren kungiyar kasuwar, Kwamaret Rabi’u Abubakar Tumfafi ne, ya bayyana haka ga manema labarai a madadin kungiyar kasuwar cikin wata sanarwa daya fitar.

 

Kwamarat Rab’iu Abubakar Tumfafi, yace shugabancin kungiyar kasuwar a kodayaushe yana iya kokarinsa wajen ganin ta bijiro da managartan ayyuka da tsare_tsaren da za su bunkasa harkokin kasuwancin yan kasuwa domin su yi gogayya da sauran kasuwanni na Duniya.

2023:Ka kula da lafiyarka, domin kamfedin bana Mai wuya ne – Kwankwaso ya fadawa Tinubu

Kamar yadda aka Sani Mutanenmu suna fitar da kayayyakin da suka shafi Abinci kamar su waken suya da wake da Shinkafa da masara da gyada da Ridi da dai sauran na’u’ikan kayan gona Wanda da sune Najeriya ta kafu kafin a samu man fetur a Shekarun da suka gabata”. Inji Tumfafi 

Hawan Nasarawa:Ganduje ya bayyana dalilin da yasa bai tarbi Sarkin Kano a gidan gwamnatin ba

Yace sabon shugabanci kasuwar Dawanau, a shiye yake wajen ganin ya hada hannu da kamfanoni masu zaman Kansu na Gidan Najeriya da kasashen ketare domin ganin kasuwancin al’ummar kasuwar ya kara habaka fiye da yadda yake a baya.

 

Zamani ya zo da sauye_sauye daban_daban da ya kamata al’ummar mu su fahimci wannan sauyin da duniya ta zo da shi , domin inganta harkokin kasuwancinsu”.

 

Yace yana amfani da wannan da ma wajen yin kira ga al’ummar kasuwar, da su ci gaba da baiwa kungiyar hadin kan daya dace domin ganin an samu nasarar da aka sanya a gaba,musamman saboda managartan tsare-tsare da sabon shugabancin ya zo da su a halin yanzu.

 

Sakataren kungiyar kasuwar, ya bukaci al’ummar musulmin kasar nan, da su yi amfani da wannan lokaci wajen sanya kasar nan a cikin addu’o’in yau da kullum, domin ganin an samu saukin mawuyacin halin da yan kasa suka samu Kansu a cikin .

 

Haka zalika yace shugabancin kungiyar kasuwar, yana taya Gwamnati jihar Kano da ta karamar hukumar Dawakin Tafa murnar sallah Babba da daukacin al’ummar Najeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...