Hawan Nasarawa:Ganduje ya bayyana dalilin da yasa bai tarbi Sarkin Kano a gidan gwamnatin ba

Date:

Daga Halima Umar Sabaru

 

Gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske kan rashin halartar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero gidan gwamnati domin halartar bikin Hawan Nasarawa a ranar Litinin a wani bangare na bukukuwan Babbar Sallah.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan, cikin wata sanarwar da ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24, inda ya bayyana cewa Gwamna ne ya tafi abuja domin halartar wani taron gaggawa Mai matukar muhimmanci wanda ya zama wajibi ya halartar wanda za’a tattauna al’amuran kasa masu muhimmanci a ranar litinin din nan.

 

Ya ce Gwamnan ya halarci Sallar Idi tare da Sarkin a filin Idi na Kofar Mata, sannan ya tarbe shi daga bisani a Gidan Shattima sannan kuma ya halarci bikin Hawan Daushe a fadar Sarkin Kano da yammacin ranar Lahadi, kafin ya wuce Abuja da yamma don halartar Wani taron gwamnoni wanda babu damar tura wakili.

Muhammad Garba ya kara da cewa bayan ganawarsu, an kuma shirya gwamnonin za su yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin sakamakon zaman nasu a gobe talata .

2023:Ka kula da lafiyarka, domin kamfedin bana Mai wuya ne – Kwankwaso ya fadawa Tinubu

Kwamishinan ya kara da cewa mutane biyun da ya Kamata su wakilci Gwamnan wajen tarbar Mai Martaba Sarkin ba tare da an karya ka’idar ba, sune mataimakinsa, Dakta Nasir Yusuf Gawuna ko shugaban majalisar dokokin jihar, Hon.Hamisu Ibrahim Chidari, wadanda dukkaninsu basa kasar nan sun kasa Mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.

Ya bayyana cewa, sauran jami’in da zai iya wakiltar wadannan mutane tsayawa ukun, shi ne sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, wanda kuma shi ne Wazirin Gaya, mai rike da sarautar gargajiya a karkashin Masarautar Gaya wanda bashi damar tamkar rashin girmamawa ne ga Mai Martaba Sarkin dama al’adar hawan baki daya.

Ganduje ya yiwa fursunoni sama da 3,800 afuwa cikin Shekaru 7

Kwamishinan ya yi nuni da cewa tun kafin ya yi tafiyar, gwamnan ya tattauna da sarkin kan sabon ci gaban da aka samu, kuma dukkansu sun amince cewa ba za a yi ziyarar Sallah ba, amma sarkin zai gabatar da hawansa kamar yadda ya Saba ba tare da ya shiga gidan gwamnatin ba.

Muhammad Garba ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa gwamnan ya wulakanta Sarkin, Inda yayi kira ga jama’a da su yi watsi da labarin domin bashi da tushe ballantana Makama wanda zasu marasa kishin kano suke yadawa don kawo rudani a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...