Daga Rahama Umar Kwaru
Dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa/Tofa da Rimingado a Majalisar Wakilai, Honorabul Tijjani Abdulkadir Jobe ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin su
Honarabul Jobe a cikin sakonsa na Barka da Sallah da ke kunshe A cikin wata sanarwa, ya ce zaman lafiya da hadin kai su ne ginshikin ci gaban kowacce irin al’umma.
Jobe ya kara da cewa Najeriya a matsayinta na kasa mai kabilu daban-daban ta na bukatar zaman lafiya da hadin kai don samun ci gaba.
2023:Ka kula da lafiyarka, domin kamfedin bana Mai wuya ne – Kwankwaso ya fadawa Tinubu
“Zaman lafiya da hadin kai sune muhimman abubuwan da ake bukata domin ciyar da kasar nan gaba. Duk yadda shugabanni za su kasance nagari, idan babu zaman lafiya da hadin kai ba za a iya cimma abun da ake bukata ba”.
“Al’ummar da ke da kabilu da kabilu iri-iri kamar Najeriya ba za ta taba samun ci gaba ba sai da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummarta. Don haka ya kamata mu yi amfani da bambance-bambancen mu don ci gaban al’ummarmu.
Dan takarar Gwamnan Kano a P R P ya yiwa al’ummar musulmi barka da sallah
“Kowace kabila a kasar nan na da wani abu na musamman da za ta ba da gudunmawa wajen bunkasa kasar. Don haka idan muka hada kawunanmu ne kawai za mu iya amfani da karfinmu don ci gaban kasa,” inji shi.
Hon. Jobe ya yi kira ga al’ummar musulmi da su yi riko da kyawawan dabi’u na Musulunci da kuma samar da zaman lafiya da hadin kai a mu’amalarsu da mabiya sauran addinai.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasa ya basu ta hanyar kammalakar katin zabe na dindindin, inda ya ce karbar katin zaben ya zama dole domin idan ba tare da shi ba babu wanda zai iya yin zaben da ke tafe.