Daga Rukayya Abdullahi Maida
Tsohon babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar tarayya, Hon. Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila ya taya al’ummar musulmi murnar Babbar Sallah.
Hon. Sumaila ya bayyana hakan ne a sakonsa na Barka da Sallah ga al’ummar jihar kano da kasa baki daya, inda ya yi fatan al’ummar Musulmi murnar gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
Hon. Kawu Sumaila Wanda shi ne dan takarar Sanatan Kano ta kudu a jam’iyyar NNPP ya bukaci al’ummar musulmin da su kasance masu hakuri da son juna musamman a lokutan da suke mu’amala da mabiya wasu addinai, a cewarsa akwai bukatar ‘yan Najeriya su hada kai ba tare da la’akari da banbancin addininsu ba don ciyar da kasar gaba.
2023: Wani Malami a Kano ya yi tallan Kwankwaso a filin Sallar idi
Ya kuma hori musulmi da su kiyaye kyawawan dabi’un da Musulunci ya koya musu ta yadda za su zauna lafiya ba kawai da ‘yan uwa musulmi ba, har ma da mabiya sauran addinai.
Sumaila ya kara da cewa, ba za a iya samun zaman lafiya da hadin kai a Najeriya ba, in ba tare da hakuri a tsakanin mabiya manyan addinai biyu na Musulunci da Kirista ba.
Da dumi-dumi: Tinubu ya amince zai dauki Mataimaki Musulmi a zaben 2023
Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, ya bukaci ‘yan Najeriya da su karbi katin zabe, yana mai cewa “Samun katin zabe abu ne mai muhimmanci ga kowane musulmi. Da shi ne kawai za ku iya zabar shugabannin da kuke so wadanda zasu kawo muku cigaba ta kowacce fuska”.
“Wannan dama ce a gare ku ku zabi shuwagabanni na gari ku maye gurbinsu bars gurbi da nagartattun shugabanni. Idan ku ka rasa wannan damar , ba za ku iya zaɓar shugabanni na gari ba shekara ta 2023 .
“Lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su hada kai don yakar munanan shugabanni kuma daya daga cikin hanyoyin cimma wannan gagarumin aiki shi ne ta hanyar karbar katin zabe na dindindin.
“Bai kamata al’ummar musulmi su yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da gudunmawar kason su don samar da managartan shugabanni a kakar zabe mai zuwa.