2023: Wani Malami a Kano ya yi tallan Kwankwaso a filin Sallar idi

Date:

 

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Daawah a Kano, Sheikh Muhammad Aminuddeen, ya buƙaci ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya ƙara himma a kan takarar sa ta neman shugabancin ƙasar nan.

Babban limamin, wanda ɗan marigayi shahararren malamin addinin Musuluncin nan ne a Kano, Sheikh Aminuddeen Abubakar, wanda ya kafa Gidauniyar Daawah Group of Nigeria.

Da ya ke gabatar da huɗuba bayan an idar da sallar idi ga dubban masallata da suka hada da Kwankwaso a yau Asabar, limamin ya ce tsohon gwamnan jihar Kano “yana da dukkan kyawawan halaye da zai jagoranci Najeriya kuma ya fi sauran ƴan takarar shugaban kasa na APC da PDP.”

Ya lura cewa MKwankwaso “yana matukar son ci gaban Najeriya”.

Shehin Malamin ya kara da cewa tsohon ministan tsaron abokin mahaifinsa ne, marigayi Sheikh Aminuddeen wanda ya rasu a shekarar 2015.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kuɓutar da Nijeriya daga kalubalen tsaro da ake fama da shi, Ya kuma yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari jagora ya jagoranci kasar nan cikin nasara.

Daily Nigerian ta rawaito Sallar ta kuma samu halartar ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf da abokin takararsa Kwamared Aminu Abdussalam da sauran manyan baƙi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...