Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace addu’o’in da malamai suke yiwa jihar nan ne yasa jihar tafi kowacce jiha Zaman lafiya a duk fadin Nigeria.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin addu’o’i na musamman da gwamnatin jihar kano ta Saba shiryawa a duk ranar arfa domin rokon Allah ya kara inganta Zaman lafiyar da ake da shi a jihar kano da kasa baki daya.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa tana shirya addu’o’in ne a irin wannan Rana ta arfa saboda Rana ce da Allah yake amsa addu’o’in bayinsa, saboda a rokawa kano Zaman lafiya da karuwar tattalin arziki.
“Duk wani mugu a ko’ina yake indai ya shigo jihar Kano Allah Yana baiwa jami’an tsaro ikon kama shi, to wannan na faruwa ne sakamakon yadda Malaman jihar nan suke dagewa da yin addu’o’in ba lallai a irin wannan lokaci kadai ba har da sauran lokutan karatu da sallolin farilla dana nafila”.Inji Ganduje
Yace Dan Adam baya sanin muhimmancin Zaman lafiya sai lokacin da ya tsinci kansa a cikin yanayi na Rashin Zaman lafiya, don haka ya bukaci al’umma su himmatu wajen yin addu’o’in samun Zaman lafiya.
Gwamnan Ganduje ya kuma yabawa malaman bisa addu’o’in samun nasara da suka yiwa mataimakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna wanda shi yake yiwa jam’iyyar APC takarar gwamna da kuma Dan takarar shugaban kasa a APC Alhaji Bola Ahmad Tinubu domin su sami nasara a zaben shekara ta 2023.
Mu muka baiwa Tinubu shawar ya dauki Mataimaki Musulmi, kuma ya Amince – Ganduje
Malamai da dama ne dai daga kowanne bangaren Izala, Kadiriyya da Tijjaniyya suka gudanar da saukar al’qur’ani Mai girma tare da yiwa jihar Kano da Nigeria addu’o’in samun Zaman lafiya da karuwar tattalin arzikin kasa.