Zaharadeen saleh
Kungiyar kwallon kafa ta kano pillars ta samu nasarar doke kungiyar Nasarawa united daci daya da nema a cigaba da gasar cin kofin kwallon kafa ajin firimiya ta Nigeria, zagayen wasa mako na 23 da aka fafata a laraban nan.
Dan wasan kungiyar kano pillars, Auwalu Ali malam ne ya samu nasarar jefa kwallo daya tilo araga a mintina 25 da fara wasan wadda ya kano pillars din nasara wasan.
Yanzu haka bisa nasarar da kano pillars ta samu ta dawo matsayi na daya da maki 44 daga wasanin 23 data buga.
Ga sakamakon ragowar wasanin mako na 23.
Wikki Toursts 1 Vs Enyimba 2
Adamawa utd 1 Vs Katsina utd 0
Kwara utd 1 Vs Rivers utd 1
Dakkada fc 2 Vs fc Ifeanyi 1
Warri wolves 1 Vs Lobi 0
Sunshine 0 Vs MFM fc 0
A safiyar Alhamis din nan da misalin karfe 8 na safe za’a kara wasa tsakanin
Heartland fc v Plateau utd
Sai da misalin karfe 4 na yamma a ranar 17/05/2021 za’a kara tsakanin
Abia w. Vs Akwa utd fc
Enugu Rangers Vs Jigawa G. Stars fc