Ganduje Zai Samar da Cibiyoyin Adana Madarar Shano guda 200 a fadin jihar Kano

Date:

Daga Muhd Sale Hotoro


 Shirin bunkasa kiwo na makiyaya na jihar Kano, KSADP, ya ba da kwangila don tsarawa da kulawa da ayyukan tuntuba don kafawa da kula da cibiyoyin tattara madara har 200 a fadin kananan hukumomin 44 na jihar.  


Kadaura24 ta rawaito an ba da kwangilar ne ga kamfanin Messrs Teamwork Global Associates, wani kamfani na Yan  asali Jihar nan.


 Haka kuma, Shirin ya sanya hannu kan kwangilar tsarawa da kula da tuntuba don gina dakin gwaje-gwaje na likitocin dabbobi a Kundila, karamar hukumar Tarauni.  An bayar da wannan Aiki ga Kamfanin Kul-Dwell Consultants Ltd.


Jami’in yada labaran Shirin Ameen K. Yassar yace Kwangilolin za su hada da ayyukan Masu bada shawarwari, samar da ma’aikata bada horo da samar da taswirar da Samar da wurare daban-daban da ake son samarwa, da dai sauransu.


 Jami’an ba da shawarar za su ba da shawarar yadda za’a aiwatarwa da ayyukan dai-dai da sharuɗɗan da aka amince da su yayin yarjejeniyar.


 Da yake jawabi jim kadan bayan sanya hannu kan kwangilar, Babban Jami’in Gudanar da Shirin na Jihar Ibrahim Garba Muhammad ya ce: “Ainihin, wannan Shirin yana da niyyar gabatar da sabbin dabaru a cikin Aikin Samar da madara a jihar Kano da Kuma yadda za’a inganta tsarin ta Hanyar fasahar zamani”.


 A sakamakon haka, “KSADP na shirin gina cibiyoyin tattara madara tare da kayan aiki na zamani, tare da samar da Na’urar sanyaya madarari wanda zai haifar da karuwar bukatar kayayyakin kiwo, karuwar farashin madarar da, magance Matsaloli da batutuwan ingantar madara da Kuma  tsaftaceta”, Ibrahim Garba ya jaddada.


Babban Jami’in kula da Shirin ya ce dakin gwaje-gwajen kiwon lafiyar dabbobi yana daya daga cikin shirye-shirye da dama da aka gabatar da nufin bunkasa lafiyar dabbobi, da tabbatar da lafiyar abincin da dabbobin ke samu da kuma kiyaye lafiyar jama’a gaba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...