Daga Zakaria Adam Jigirya
Hukumar kidayar jama’a ta kasa ta ce Zata fara gudanar da kidayar gwaji a ranar 11 ga wannan wata na yuli domin sanin makamar yadda za’a kidayar a shekara ta 2023 kamar yadda aka tsara .
Shugaban Hukumar a Kano Dr. Isma’il Lawan Sulaiman ne ya bayyana hakan yayin taron wayar da kan masu ruwa da tsaki a yankin Kano ta kudu kan yadda za’a gudanar da aikin kidayar a yankin.
Dr. Isma’il Lawan yace an shirya taron ne domin a wayar da Kan Masu ruwa da tsaki, wadanda suka hadar da Dagatai, Masu unguwanni limamai da dalibai domin su fahimci muhimmanci kidayar gwaji don a sami hadin kan da ake nema daga al’ummar yankin.
Yace za’a gudanar da kidayar gwajin ne domin a fahimci yadda za’a gudanar da aikin da kuma yadda za’a magance kalubalen da za’a fuskanta gabanin fara ainahin kidayar da za’a yi a shekara Mai zuwa.
kwamishinan hukumar yace zasu gudanar da kidayar gwajin ne a kananan hukumomin 9 dake shiyyoyi uku na jihar Kano, kuma tuni an kammala bada horo ga wadanda zasu gudanar da aikin.
A nasa jawabin Hakimin Rano Alhaji Kabiru Ibrahim wanda Dagachin Madaci Alhaji Ado Ibrahim bayan ya yabawa hukumar ya kuma bada tabbacin zasu bada duk wani hadin kai da ake da bukata domin samun nasarar aikin.
Hakimin na Rano ya kuma hori Dagatai da masu unguwanni da sauran al’ummar da za’a gabatar da aikin a yankin su zamo Masu bada hadin kai don a sami nasara, sannan yace zasu dauki mataki Mai tsauri akan duk wanda ya ki bada hadin kai ga jami’an da zasu gudanar da aikin kidayar gwajin.
Shi ma a jawabinsa shugaban karamar hukumar Rano Ruwan kanta ya bada tabbacin karamar hukumar Zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samin nasarar da ake fata, ta hanyar bada gudunmawar ta konne fanni.
Za dai a gudanar da kidayar gwajin ne a kananan hukumomin Rano Kibiya da bunkure dake yankin Kano ta kudu a jihar kano.