Daga Kamal Yahya Zakaria
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta Nemi afuwar Maniyatan Nigeria na bana dangane da wahalhalun da suka Sha yayin jigilar maniyatan daga Nigeria zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ibadar aikin Hajjin bana.
Kadaura24 ta rawaito Cikin wata sanarwa da jami’ar yada labaran hukumar NAHCON Fatima Sands Usara ta fitar tace Hukumar ta kuma Nemi afuwar gwamnatin tarayyar Najeriya, da hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, masu kamfanonin jirgin yawo, sauran jama’a kan duk abubuwa marasa dadi da suka faru a makonnin da suka gabata.
Abin takaicin shi ne, duk da kokarin da aka yi na jigilar dukkan maniyyatan Najeriya da ke sda niyyar zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2022, NAHCON ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman sakamakon koma bayan da aka samu a karshen makon da ya gabata, wanda ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar maniyyatan zuwa ranar 27 ga watan Yuni na wannan shekara. “Sai dai abin takaicin shi ne, yadda kamfanonin jirgien da muka zaba kuma suka bamu tabbacin zasu iya wannan aikin Amma su ne sular duk wadannan matsaloli da muka samu na kasa kammala jigilar dukkanin maniyatan kasar nan zuwa kasa mai tsarki.
Musamman, wadannan adadin maniyyatan da abin ya shafa ba sune muka gaza kaisu kasar saudiyya har lokacin rufe filin jirgi sama na jidda ,wanda hakan ya tabbatar da cewa sun rasa aikin Hajjin na bana. akwai maniyatan tara (9) daga jihar Bauchi; maniyatan 91 daga jihar Filato; Maniyata 700 ne daga jihar Kano da kuma mahajjata kimanin 750 daga bangaren masu bin jirgin yawo.
Sanarwar tace Hukumar ta ba da tabbacin cewa za a mayar wa dukkan maniyyatan da abin ya shafa kudin aikin Hajjinsu yayin da za ta yi kokarin gyara matsalolin da a nan gaba.
NAHCON ta koyi darussa da dama kuma ta kuduri aniyar ganin hakan bata a sake faruwa ba, Hukumar bata da kalmomin da zata yi amfani dasu wajen hakurkurtar da yan Nigeria musamman wadanda suka kudiri aniyar aikin Hajjin sakamakon mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.