Gwamnatin Katsina ta tabbatar da bullar cutar Kyandar Biri a jihar

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

An samu bullar cutar Kyandar Biri a Katsina kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

 

Gwamnatin ta tabbatar cewa cutar ta harbi mutum daya yayin da ake dakon sakamakon wasu samfura 15 daga dakin gwaje-gwaje da aka kai Abuja, babban birnin kasar nan.

 

Kwamishinan Lafiyar jihar, Yakubu Nuhu Danja ne ya tabbatar da hakan ranar Talata, yayin kaddamar da shirin rarraba magunguna kyauta da kuma cibiyar kiran nema agajin gaggawa a Ofishin Hukumar Lafiya a Matakin Farko na jihar.

 

Mu fito mu Tsaftace Muhallanmu don gujewa ambaliyar ruwan sama – Falakin Shinkafi

 

“Mun tabbatar da cewa cutar kyandar biri ta harbi mutum daya kuma an dauki dukkan matakan da suka dace na yi wa marar lafiya magani da tuni an sallame shi.

 

“Muna da wasu mutum 15 da aka zargin sun kamu da cutar wadanda aka kai samfurin jininsyu dakin gwaje-gwaje da ke Abuja.

 

 

 

“A yanzu haka muna sa ran sakamakon gwaje-gwajen zai fito nan da mako guda,” a cewarsa.

 

Duk da karin lokacin jigila, maniyyatan Najeriya 8,000 za su iya rasa Hajjin bana

 

Daily News24 ta rawaito dangane da aikin rarraba magunguna da gwamnatin jihar ta kaddamar, Kwamishinan ya ce hakan wani mataki na tunkarar yiwuwar barkewar cututtuka da galibi akan samu a irin wannan lokaci na damina.

 

“A yanzu haka mun tanadi rigakafin magance annobar cututtuka irinsu cutar Sankarau, Kyanda da Kwala.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...