Daga Abubakar Dayyabu Safana
Majalisar Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Hauwan bukukuwan Sallah Babba a ranar Asabar.
Sanarwar dakatarwar ta fito ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Katsina, Mai dauke da sa hannun mataimakin sakataren majalisar, Sule Mamman-Dee.
Ya ce an dakatar da hawan ne saboda yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar.
A cewar Mamman-Dee, Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna matukar damuwarsa kan matsalar tsaro a sassan masarautar inda ya ce zai halarci Sallar Idi ne kawai a ranar Asabar ba tare da hawan sallah ba.
Ya bayyana cewa Sarkin ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Bikin Durbar dai ya samo asali ne tun shekaru aru aru da suka gabata, Shekaru kusan biyu kenan ba’a gudanar da hawan ba, saboda matsala ta tsaro data addabi al’ummar jihar.