Dan takarar Gwamnan APC a Kaduna ya sake zabar Mace a matsayin mataimakiyar sa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, Sen Uba Sani ya zabi Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2023.
 Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa Uba Sani ya fitar ranar Litinin kamar yadda jaridar solacebase ta rawaito.
 “Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina mai farin cikin sanar da cewa na zabi mai girma mataimakiyar Gwamna, Dokta Hadeeza Balarabe a matsayin abokiyar takarata a zaben gwamna na 2023 a jihar Kaduna,” in ji sanarwar.
Majiyar Kadaura24 ta ruwaito cewa Hadiza Sabuwa Balarabe, ita ce mataimakiyar gwamnan Nasir El-Rufai a halin yanzu
 “Dr.  Hadiza Balarabe ta ba da gudunmawa sosai ga gagarumin ci gaba da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu a fannin samar da ababen more rayuwa da ci gaban jama’a a jihar.
 “Dr.  Balarabe ta nuna kwazo sosai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na mataimakiyar Gwamna wanda ya kara mata daraja a cikin masu ruwa da tsaki a jihar.
 Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Don haka ina kira ga al’ummar jihar Kaduna da su goyi bayan zabin Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata.  Na kuma bukace ku da ku fito ranar zabe don kada mana kuri’a yayin babban zaben 2023 mai zuwa. Zabar mu a 2023 zai ba mu damar gina jihar Kaduna cikin lumana, wadata, da kuma girma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...