Daga Rukayya Abdullahi Maida
Jirgin Max Air ya kwashe sama da sa’o’i hudu a filin jirgin saman birnin Khartoum na kasar Sudan tare da Maniyatan jihar Neja.
Kadaura24 ta rawaito Kawo yanzu dai babu wani dalili da ya sa jirgin ya sauka a birnin Khartoum kafin ya wuce birnin Jeddah na kasar Saudiyya.
Jirgin Mai kirar Boeing 747-4B5/B744 da ke karkashin kamfanin Max Airline ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe tare da Maniyatan Nijar 544 da jami’ai 16 da karfe 10:53 na ranar Lahadi.
Sai dai a maimakon tafiyar sa’o’i hudu da rabi zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah, jirgin Max Air mai lamba 5N-HMM ya kwashe sama da sa’o’i 9. Kamar yadda rahoton Hajj Reporters ya nuna
Wani jami’in kamfanin jirgin da ya ki bayyana sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai kan lamarin ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce jirgin Max Air mai lamba VM1051 “ya bar Abuja da karfe 20:53 agogon GMT a ranar 3 ga watan Yuli kuma ya sauka a Khartoum da karfe 02:33 agogon GMT a ranar 4 ga watan Yuli.”
Ya ce jirgin ya shafe sa’o’i 4 na mintuna 26 a filin jirgin saman Khartoum tare da Maniyatan Nijar. Sai dai ya ki bayyana babban dalilin da ya sa aka tsayar da jirgin a Sudan Maimakon jidda.
HAJJ REPORTERS ta ruwaito cewa jirgin Max Air ya isa Jeddah ne da safiyar Litinin din nan.
Wani jami’in ya ce jirgin Max Air “ya tashi daga Khartoum da karfe 6:59 agogon GMT a ranar 4 ga Yuli kuma ya isa Jeddah da karfe 8:22 na safe a ranar Litinin.”
Daya daga cikin mahajjatan, wacce ta bayyana kanta a matsayin Maman Muhamad, ta shaida wa manema labarai cewa abin da ya same su abun takaici ne . Mun yi kwanaki a sansanin Hajji na Minna kafin a kai mu Abuja domin a yi jigilar mu. Jami’an Max Air ba sa girmama fasinjojinsu. Sun yi mana mugun hali a cikin jirgin sai da mukai sa’o’i 10 a jirgin.”
Wannan lamari dai ya kara zurfafa radadin da kashin farko na alhazan Nijar da suka shafe kwanaki a sansanin Hajjin Minna kafin a kai su Abuja don yin balaguro.