Za a gudanar da aikin Hajjin bana cikin tsananin zafin Rana – Masana

Date:

Daga Rahama Kwaru

 

Cibiyar Kula da Yanayi ta Kasar Saudiyya (NCM) ta ba da rahoton cewa ana sa ran samun zafi Mai yawa a wurare masu tsarki a lokacin aikin Hajjin shekarar 2022 Inda zafin zai kai tsakanin digiri 42-44.

Cibiyar ta ce Haramin na iya kasancewa cikin yanayin iska da rana.

Sannan kuma binciken nasu ya nuna cewa Isa da kura ka iya tasowa, wadda gudun ta ya zai kai kilomita 35 a cikin sa’a guda, musamman a wuraren da suke budaddu ne da kuma manyan tituna a birnin na Makka.

” iskar Zata taso ne daga arewa maso yamma zuwa yamma,” in ji NCM.

Cibiyar ta ce akwai yiwuwar samun ruwan a kudancin yankin Makkah daga ranar 9 zuwa 13 na Dhu Al-Hijjah, wanda zai iya shafar wurare masu tsarki tare da iska mai ƙura.

A Cikin wani littafi da Al-Mashaer Bulletin, ya rubuta wanda ma’aikatar aikin Hajji ta buga a shekara ta 1429 bayan hijira mai taken Rabe-raben shekarun Hajji daga shekara ta 1201H zuwa 1500 bayan hijira, ya bayyana cewa Hajjin bana zai kasance aikin hajjin da mahajjata za su gudanar da ayyukan ibadar su a lokacin bazara.

Yanzu shekaru 7 kenan a jere ana aikin Hajjin cikin bazara, wanda ya fara tun a shekara ta 1437 bayan hijira kuma zai kare a lokacin aikin Hajji na shekara ta 1444 bayan hijira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...