Daga Aisha Aliyu Umar
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar saudiyya, ta amince da tsawaita izinin sauka ga masu jigilar alhazan Najeriya a karkashin inuwar hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON daga yau 4 ga wata zuwa 6 ga watan yuli da muke ciki domin baiwa Hukumar damar karasa kwashe maniyatan kasar nan zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajji bana.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar yada labaran hukumar NAHCON Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Abuja.
Hukumar NAHCON ce dai ta bukaci karin wa’adin domin ta samu damar jigilar sauran mahajjatan da suka rage cikin mahajjata 43,008 da ake sa ran za su sauke farali a bana,Amma a cikin su yanzu haka maniyatan Najeriya, 27,359, da suka hada da ma’aikata 527 da kwamitoci da shuwagabannin hukumar, sun Isa kasar saudiyya . Hakazalika, sama da maniyatan 5,000 daga cikin mahajjatan jirgin yawo 8,097 suma sun Isa kasar ta saudiyya.
“Neman tsawaita lokacin ya zama wajibi ne sakamakon soke tashin wasu jirgi da ya wuce kima da kuma jinkirin tashin wasu jiragen da aka samu. Bayanai sun nuna cewa, daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Yuni, an soke tashin jirage 9 saboda dalilai da suka hada da gaza samar da kudin guzuri, rashin isassun kudade na biza, rashin samun sakamakon gwajin PCR da dai sauransu”.
Sanarwar ta ce duk da wannan mawuyacin hali, NAHCON ta sake nanata cewa in Allah ya yarda, babu wani mahajjaci da za a bar shi a kasa ba, matukar yana da ingantattun takardun tafiya. yace don tabbatar da hakan a jiya sawu 7 Akai wanda hakan ya karu akan yadda ake jigilar a baya ta” Alhamdu lillahi, daya daga cikin ikon Allah jirgin FlyNas zai rika yin sawu 4 a kowacce rana, Inda zai rika kwasar mahajjata 1,732 a kowacce rana.
sanarwar tace NAHCON ta yi kira ga maniyyata da su kwantar da hankulansu kuma su kasance cikin shiri don isa kasar saudiyya domin gudana da aikin Hajjin 2022. Hukumar ba ta ji dadin duk wani tashin hankali da damuwa da mahajjata suka fuskanta ba yayin wannan tafiya ta ibada zuwa kasa mai tsarki.
shugaban Hukumar ta NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya yabawa Alhazan Najeriya bisa juriyar da suke nunawa tare da yi musu addu’ar Allah ya kaisu aikin Hajji kuma su yi karbabbe wanda ladansa shine jannatul Firdausi. Ya ba da tabbacin cewa hukumar NAHCON za ta sake duba ayyukan don tabbatar da cewa ba a sake samun irin wannan matsala ba.