Daga Safyan Dantala Jobawa
Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Musanta zargin da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i yayi na cewa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya baiwa Kungiyar Kwadagon kudi domin su yi masa Zanga-zanga a kaduna.
Cikin Wata Sanarwa da Kadaura24 ta samu Mai dauke da sa Hannun Shugaban Kungiyar Kwadagon ta Kasa Comrade Ayuba Wabba, yace Ganduje bashi da Hannu ta kowacce fuska akan Zanga-zanga da muka gudanar.
Sanarwar tace Kungiyar ta gudanar da Zanga-zangar ne kawai Saboda yadda Gwamna Nasir El-Rufa’i yake cisgunawa Ma’aikata a jihar da Kuma yadda yake korarsu Daga aiki ba gaira Babu dalili.
“Mun ci Karo da Wani video da ya nuna Gwamna Nasir El-Rufa’i Yana zargin Ganduje da bamu kudi domin muyi Zanga-zanga,Ina so El-Rufa’i ya sani Kungiyar mu Bata yarda Wani ya shigo Cikinta har ya Bamu kudin don muyi Wani abu”. Inji Wabba
Sanarwa tayi Kira ga jama’an Tsaro da su Sanya idanu domin gudanar da aikin su yadda ya dace Saboda yadda El-Rufa’i yake yiwa Ma’aikatan da Kungiyar Kwadago baraza, Inda yace Barazanar sa bazata Hana Kungiyar neman Hakkin ‘ya’yanta ba.
Daga Karshe Ayuba Wabba a Cikin sanarwar yace Kungiyar su kowa ya santa da dattako da gudanar da aiyukanta akan tsare, yace zasu tabbatar sun ci gaba da kasancewa akan Wannan Matsayi domin Kare Martaba da Mutincin Ma’aikata a Kasar nan