Babu Aure Tsakanina da Sani Danja-Mansur Isah

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Suleman

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Mansura Isa ta bayyana cewa a yanzu haka babu aure a tsakaninta da mijinta Sani Musa Danja wanda ya ke fitaccen jarumi ne shi ma a masana’antar Kannywood.

Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Mansura Isan na bayyana hakan a shafinta na Instagram minti guda kafin ta goge rubutun.

A zantawar da mu ka yi da mijin nata, Sani Danja ta wayar salula, mun tambaye shi ko shin gaskiya ne sun rabu da matarsa Mansura Isah ? Sai ya amsa da cewa:”Ku je ku tambaye ta tunda ita ce ta rubuta”. Cewar Sani Danja.

Sai dai kuma wata majiya mai tushe wacce ta nemi mu sakaya sunanta ta tabbatar mana da cewa auren na Sani Danja da Mansura Isah ya daɗe da mutuwa yau tsawon shekara ɗaya kenan ba sa tare a matsayin miji da mata.

Sani Danja da Mansura Isah fitattun jarumai ne masu tashe a masana’antar Kannywood waɗanda su ka yi aure irin na soyayya tsawon shekaru kusan goma da su ka gabata. Yanzu haka su na da ƴaƴa hudu mace ɗaya da maza ukku waɗanda su ka haifa tare kafin su kai ga datse igiyar auren da ke tsakaninsu.

Kadaura24 ta rawaito Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto mun yi ta ƙoƙarin tuntuɓar Jaruma Mansura Isah ta wayar salula domin jin ta bakinta game da gaskiyar wannan lamari da ta rubuta ta goge, mun sameta amma Bata Bata Daga wayarmu ba.

74 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...