Dr. Dauda Lawan zai gabatar da Makala a taron masana harkokin kudin a kasar Burtaniya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a tutar jamo PDP Dr. Dauda Lawan wanda kuma shi ne mataimakin shugaba kuma mamallakin kamfanin Credent Capital & advisory Limited zai gabatar da jawabi a wajen wani taron kwararru kan harkokin banki a duniya mai taken 2022 Reputable Banks and Fintech Awards/Conference (RBFA) a Glasgow, wanda za’a gudanar a Glasgow dake bKasar Ingila .

 

Wadanda suka shirya taron sun ce an zabo Dr. Dauda Lawan Phd ne domin ya gabatar da jawabi a wajen taron saboda kwarewa gogewar,Ilimi, da yake da ita a harkokin da suka shafi sha’anin banki da kudaden.

 

An shirya taron ne domin a tsara yadda faɗaɗa, haɓaka, da kuma sauya fasalin ɓangaren harkokin kudi a Afirka.

Talla

 

Beldina Auma guda ce cikin shugabannin taron kuma ita ce tsohuwar Shugaban kungiyar ma’aikatan bankin bada lamuni na duniya dake africa tace taron RBFA na 2022 za’a gabatar da tattaunawa da muhawara da manyan malamai daga Afirka da Turai wadanda zasu baje kolin kwarewa kan yadda sassa daban-daban za su iya yin aiki tare don haɓaka hada-hadar kuɗi. Manyan masu ruwa da tsaki za su hadar da bankuna, inshora, masu ba da gudummawa, masu saka hannun jari, masu tsara manufofi, da masu gudanarwa.

 

Dr. Dauda Lawan dan takarar gwamnan jihar Zamfara a PDP

Dr. Dauda Lawan dan takarar gwamnan jihar Zamfara a PDP

 

Masu shirya RBFA sun ce Dauda Lawal, Ph.D. An zabi tsohon babban darakta a bangaren gwamnati, First Bank Nigeria Limited domin ya zama shugaban majalisa a RBFA da taro bisa la’akari da dimbin gogewarsa, ilimi, gwaninta, da fasaharsa a cibiyoyin hada-hadar kudi.

 

 

 

An yi kyakyawan tunani matuka wajen zabo wadanda zasu halasci taron ne na shekara ta 2022 wadanda suka shahara wajen harkokin kudin musamman a Afirka.

 

 

 

Dr. Dauda, ​​Dan Takarar Gwamnan Jihar Zamfara na Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, zai tattauna muhimman batutuwan da suka shafi cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya a yayin taron.

 

An tsara taron ne da bada lambar yabo a shekara ta 2022 a ranar Talata 28th – zuwa Alhamis 30 ga Yuni 2022 a Raddison Red, Finnieston Quay 25 Tunnel Street, Glasgow, G3 8HL, Scotland, United Kingdom.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...