Sufyan Dantala Jobawa
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Umarci Hukumar Kashe Gobara ta jiha data fara zagaye zuwa gidajen Mai dake jihar Nan domin tabbatar da cewa Na’urorinsu na Kashe Gobara Suna Aiki yadda ya kamata.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya Ziyarar Gidan Wani Gidan Mai ta Gobara ta tashi tayi sanadiyyar Jikkata sama da Mutane 70 a jihar Nan.
Gwamna Ganduje yace ya Zama wajibi kowanne Gidan Mai a jihar nan ya tabbatar Yana da Na’urorin Kashe Gobara Kuma Suna Aiki yadda ya dace.
“Duk da dai Allah ya aiko da faruwar Wannan lamari Amma da ace anyi amfani da Na’uror Kashe Gobara yadda ya kamata Wata kila da Barnard bazata Kai Haka ba”. Inji Ganduje
Yace an Samar da Na’urorin ne Saboda bacin Rana irin Wannan don Haka yace ya Zama wajibi Hukumar Kashe Gobarar ta tashi tsaye Domin tabbatar da cewa an gujewa afkuwar hakan anan gaba .
Ganduje yace za’a ci tarar Duk Wani Gidan man da aka samu bashi da Na’uror Kashe Gobarar tare da baiwa Hukumar Umarnin shirya bita ga Ma’aikatan Gidajen Mai a jihar nan dabarun yadda zasu Kashe Gobara Dama yadda zasu gobarar tashi.
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya Kuma bada tabbacin baiwa Mutanen da gobarar ta Jikkata kula ta musamman ba tare da sun biya ko sisin Kobo ba ,Sannan kuma ya Ziyarci Asibitin Murtala domin duba marasa Lafiyar