Daga Halima Musa Abubakar
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyar zata iya hukunta Asiwaju Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar na kasa, kan kalaman da ya yi akan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A lokacin da ya ziyarci Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a ranar Laraba, Tinubu ya shaida wa wakilan jam’iyyar APC cewa ba dan shi ba, da Buhari bai za zama shugaban kasa ba.
Ya ce bayan Buhari ya fadi zabe sau uku, Buhari ya yi kuka ya ce ba zai kara tsayawa takara ba, amma shi (Tinubu) yace ya je Kaduna ya roki Buhari ya sake tsayawa takara kuma zai yi nasara saboda da zasu mara Masa baya.
Wannan tsokaci dai ya janyo cece-kuce a fadin kasar nan, inda da dama ke zargin Tinubu da kamanta kansa da Allah.
Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja ranar Asabar, Adamu ya ce, “Muna iya hukunta shi (Tinubu) kan kalaman da ya yi akan Shugaban kasa.
Adamu ya kuma ce babu wani dan takarar shugaban kasa da aka haramtawa tsayawa takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da ake shirin yi ranar Litinin.