A jiya Alhamis ne wani ibtila’i , ya faru a unguwar Gandun Albasa, a layin Bala Burodo a birnin Kano, inda wata uwa mai suna Maryam Nura mai shekaru 35 da ɗanta ɗan shekara uku suka mutu sakamakon gobara da ta ƙone ginin da suke zaune a ciki. .
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi ya fitar a yau Juma’a a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a jiya Da daddare.
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 2:07 na safe daga wani Ibrahim Ashiru kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 2:11 na safe,” inji shi.
Ya ce “Ginin, gida ne mai dakuna biyar mai tsayin taku 75ft da 75ft, kuma gobarar ta rushe shi gaba daya.”
Daily Nigeria ta rawaito Abdullahi ya ce, an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne a sume kuma aka mika su ga Insfekta Shehu Lawan na ofishin ‘yan sanda na Ƙwalli, inda suka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda a nan ne kuma likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.