Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wata malama a sashin koyar da aikin jarida dake Jami’ar Bayero Kano Dr. Rukayya Aliyu ta bukaci yan jaridu da su mayar da hankali kan rahoton daya shafi bangaren lafiya da sauran batutuwa da suke faruwa a yankunan karkara, dama batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya,da nufin daga martaba kiwon lafiyar al’umma.
Dr Rukayya Aliyu ta bayyana hakan ne yayin wani taron karawa juna sani da kamfanin jaridar Solacebase ya shirya ga wasu yan jaridu hadin gwiwa da cibiyar binciken kwa-kwaf ta Wole Soyinka, da kuma gudauniyar MacArthur suka shirya, da nufin basu horo kan binciken kwa-kwaf musamman bangaren kiwon lafiya wanda aka gudanar a kano.
Kadaura24 ta rawaito Dr. Rukayya ta kara da cewa yan jarida suna da rawar takawa ta fuskar sanar da hukumomin abunda ya kamata ace sun mayar da hankali akai, baya ga batun taimakawa wajen isar da koken talakawa ga mahukunta dama sauran batutuwa da yan jarida zasu iya zama gatan mara gata.
Da yake gabatar da wata makala mai taken ‘’kariya da kuma tsaron dan jarida’’ shugaban jami’ar Kashere dake jihar Gombe Farfesa Umar Pate ya bukaci yan jaridu da suka ringa lura da sha’anin lafiyar farko kafin komai a aikin jaridar.
Karshe a nasa jawabin mawallafin jaridar Solacebase Abdullatef Abubakar Jos, yace sun shirya bayar da horon ga yan jaridu ne domin jawo hankali su zuwa ga yin rahotanni da suka shafi bangaren lafiya, da kuma bincikar yadda ake kasha makudan kudaden da akan ware domin kula da lafiyar al’umma.