Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kwamishiniyar harkokin Mata da walwalar al’umma ta Jihar Kano Dr Zahra’u Muhammad Umar ta bayyana kula da yara da Kuma basu Ilimi Mai inganci a Matsayin hanyar kyautata Rayuwar yaran a nan gaba.
Kadaura24 ta rawaito Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne yayin da take Jawabi a wajen taron tunawa da ranar Yara ta bana Wanda Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 27 ga Watan mayu na kowacce Shekara domin bikin ranar a duniya baki daya.
Tace Gwamnatin Jihar kano tana bada kulawa sosai musamman a sha’anin da ya shafi Kananan Yara domin inganta rayuwar su don su amfanar da al’umma a nan gaba.
” Gwamna Ganduje baya Wasa da duk Wani sha’ani da ya shafi Yara, Yana bamu duk abin da muka nema don kyautata Rayuwar su”. Inji Dr Zahra’u Umar
Kwamishiniyar ta kuma yi Kira ga Masu Ruwa da tsaki a ko Inna su ke dasu fito su hada hannu da gwamnatin don Kara inganta rayuwar yara a jihar Kano ko a Sami Shugabanni na gari a nan gaba.
Dr. Zahra’u Umar ta kuma yabawa mai dakin gwamnan kano Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje bisa gudunmawa da tallafin da take baiwa Ma’aikatar Mata don kyautata Rayuwar Mata da Kananan Yara a jihar nan.
“Babu abun da zamu ce da gwaggo sai godiya Saboda tana bamu Gudunmawar da bazan ma iya fadin ta ba, kuma nasan tana haka ne sakamakon tausayinta da ku yara da kuma son ganin Rayuwar ku ta inganta”. Kwamishiniyar mata
Yayin taron an shiryawa yara wasanni kala-kala domin nishadantar da su, da Kuma jawosu a jiki don su fahimci rayuwa ta Kuma bada kyaututtuka daban-daban don yabawa da gudunmawar da Waɗanda aka Karrama suke baiwa Yara da Ma’aikatar mata ta Jiha.