Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya ta baiwa El-Rufa’i Umarni

Date:

Daga Muhd Kabir

Gwamnatin Tarayya ta ce ta zata Sanya Baki  kan yajin aikin da ke gudana a Kaduna biyo bayan barazanar da ma’aikata a bangaren wutar lantarki suka yi na jefa kasar baki daya cikin duhu.


 Ministan kwadago da samar da ayyuka, Sanata Chris Ngige ya bayyana hakan a wata sanarwa da Mista Charles Akpan, Mataimakin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar ya sanya wa hannu a ranar Talata a Abuja.

 Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da (TUC) sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar wanda suka fara a ranar Litinin kan korar ma’aikata 4000 da gwamnatin Kaduna ta yi.


 Ngige ya roki gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El ‘Rufai, shugaban NLC, Com. Ayuba Wabba da shugaban TUC, Mista Quadiri Olaleye da su hau teburin Sulhu domin sasantawa Kan lamarin.


  “Muna fata kuma muna kira ga gwamnan jihar Kaduna da kar ya kara dagula lamura zuwa irin matakin da ya zama ba za a iya shawo kansa ba.


 ”Muna kuma yin kira ga shugabannin cibiyoyin kwadagon da su sauka daga aikin domin samar da hanyar tattaunawa.


 “Ma’aikata ta na shiga cikin lamarin saboda haka ta yi kira ga bangarorin da ke fada da su ba da zaman lafiya dama,” in ji shi.


  Ministan ya kuma yi kira ga dukkan ma’aikata da aiyukansu suke da muhimman ayyuka Kamar likitoci da ma’aikatan jinya da kada su shiga yajin aikin.


 Ya kara da cewa, mafi mahimmanci, ina kira ga ma’aikata a bangarori masu muhimmanci da kar su taba kayan aikin lantarki ko na ruwa domin kar jefa mutanen jihar Kaduna da ma kasa baki daya wahalhalu.

65 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...