Daga Rahama Umar Kwaru
Biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura Kuma tuni dokar ta fara aiki.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan.
Sanarwar ta ce an dauki Wannan mataki domin taimakawa jami’an tsaro don daidaita al’amura da kuma dawo da doka da oda a yankunan.
Ta kuma bayyana cewa, hukumomin tsaro na da cikakken ikon aiwatar da dokar ta-bacin, inda gwamnati ta yi kira ga daukacin mazauna kananan hukumomin Jema’a da Kaura da su baiwa jami’an tsaro hadin don dawo da zaman lafiya da bin doka da oda cikin gaggawa.
Sai dai sanarwar ta ce gwamnati ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula da kuma duk wasu ayyukan ta’addanci da suka afku a yankin, domin za a fitar da karin bayani nan gaba.