Daga Siyama Ibrahim Sani
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano a karkashin jagorancin CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi tace a kokarin ta na ganin an gudanar da bukukuwan Sallah Cikin kwanciyar hankali rundunar ta tura ‘yan sanda dubu hudu da Dari da Arba’in da Hudu (4,144) don tabbatar da tsaro a filayen Sallar Idi daban-daban da sauran wuraren a lokacin bukukuwan Sallah.
Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Rundunar DSP Abdullah Haruna kiyawa ya fitar yace Rundunar tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da sauran masu ba da agaji a jihar Kano za su yi aiki cikin tsari don tabbatar da doka da oda.
Rundunar ta shawarci masu Al’ummar Musulmi da idab za su je filin Sallar Idi su guji daukar wasu abubuwa marasa amfani wadanda za su iya haifar da zato ko fargaba.
A guji baiwa kananan yara da kuma wadanda ba su da lasisi izinin tukiyin Motoci, Babura Masu kafa uku, Babura da kuma kekuna yayin zuwa filin Sallar Idi.
Sanarwar ta Bukaci Iyaye dasu guji tura ‘ya’yansu kanana ba tare da manya ba zuwa filayen Sallar idi ko ziyartar Yan uwa Gudun gamuwa da hadari, Bata , da Sauran abubun da ba’a fata
“An shawarci mutane da su kiyaye ka’idojin Covid-19 ta hanyar sanya takunkumin da bada tazara a duk wuraren taruwar jama’a lokacin bikin.”
“Zafafan sintiri da kai samame maboyar masu aikata miyagun laifuka za su ci gaba da nufin kauce wa duk wata matsalar da za ta haifar da Rashin zaman lafiya daga masu aikata laifi da bata gari a duk fadin Jihar.”. Inji Sanarwar
Sanarwar tace Kwamishinan ‘yan sanda, Kwamandan jihar Kano, * CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi (Nagari-Nakowa), a madadin dukkan Jami’ai da Maza na rundunar suna godiya ga mutanen na jihar Kano bisa hadin kan da suke baiwa Rundunar .
Sanarwar ta Bukaci al’ummar jihar Kano dasu kirawo wadannan layukan wayar domin sanar da Yan Sanda Duk Wani motsi da basu yarda dashi ba 08032419754, 08123821575, 08075391163