Wata Gidauniya ta bada kyautar Littattafai sama da dubu ga makarantun firamare a K/H Garun Mallam

Date:

Daga Safyanu Dantala Jobawa
  Wata Ƙungiya mai suna Naziru educational foundation ta bada kyautar littattafan Karatu ga makarantun firamare don inganta sha’anin ilmi yaran yankin.
Da yake gabatar da Littattafan a gaban iyayan daliban, Shugaban Gidauniyar Comrade Naziru Dan-Hajiya Yadakwari, ya ce wannan taimakon na ɗaya daga cikin irin gudunmuwar da za su rinka bayarwa don kara inganta harkokin rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban a karamar hukumar Garun mallam.
 Ya bayyana Gidauniyar da  cewar, za ta cigaba da tallafawa Mata da Ƙananan Yara da Marasa Ƙarfi domin taimaka masu.
 “Ilimi na daya daga cikin wani ɓangaren da muka baiwa fifiko, shi yasa muka bayar da Littattafan rubutu fiye da dubu domin inganta sha’anin koyo da koyarwa a makarantunmu don inganta rayuwar’ya’yan mu”. Com. Naziru
 A nasa jawabin tsohon shugaban karamar humar Garun mallam kuma babban bako a wajen, Alh, Abdu Sule Yadakwari, ya yi bayani mai tsaho Kan muhimmancin Ilimi da kuma yadda ya kamata al’umma su rika Shiga harkokin Ilimi ta fuskar ba da tallafi a harkar.
Daga nan ya buƙaci masu hannu-da-shuni a yankin da su rinka taimaka wa a ɓangaren ilmi, domin shi kaɗai ne makamin da za’a iya magance matsalolin tsaro da shan miyagun ƙwayoyi a tsakanin al’umma.
Wakilin Kadaura24 ya ruwaito mana cewar iyayen yaran, sun gode wa shugaban wannan gidauniya ta Naziru educational foundation a bisa namijin kokarin da ya nuna a karamar hukumar Garun mallam duba da irin halin da sha’anin ilimi ke ciki a wannan karnin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...