A yau Lahadi, 13 ga watan Maris ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin babban furodusan masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da jarumar fim, Hassana Mohammed.
Kadaura24 ta rawaito auren wanda aka daura a Masallacin Murtala da ke birnin Kano, ya samu halartan manyan jaruman masana’antar wadanda suka nuna kara sosai ga abokan sana’ar tasu.
Tun farko dai labarin auren ya ja hankalin jama’a duba ga yadda ba’a cika aure tsakanin yan fim ba, domin sun fi auren yan waje, illa yan tsiraru da suka kulla auratayya a tsakaninsu.
Bayan daurin auren, Maishadda ya je shafinsa na Instagram domin nuna godiya ga Allah, inda ya yi hamdallah tare da neman masoya da su taya su da addu’a.
“ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH
“An Daura Aurena Da HASSANA MUHAMMAD. Ina bukatar addu’arku Masoya.”
Wannan aure ya dauki hankali sosai kasancewar yan masana’antar basu cika auren junansu ba.