Ra’ayin Balarabe Yaro Kurna
Watakila mai karatu ba zai gane me nake nufi ba sosai sai ya gama karanta wannan dan takaitaccen rubutun da na yi a kan Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, Damo Sarkin Hakuri.Wanda a wani lokaci can baya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce shi bai ga dan siyasa mai hakuri da juriya kamar sa ba.
Kafin ma ka je ko’ina, da wahala a ce yau akwai wani Gwamna a Najeriya da yake shan zagi da muzantawa da kage da kuma cin zarafi a kan sa da kan iyalansa, sama da Gwamna Ganduje. Kawai ya zama karkatacciyar kuka mai dadin hawa.
Duk fa rashin kyauta masa din nan da a ke ta yi masa, wanda ta kafafen sadarwa na Sada zumunta da kuma kafafen yada labarai a ke masa su, tare da kuma taimakawar wadannan kafafen yada labarai, amma har yanzu ba mu taba samun ko da sau daya ne, da a ka ce gwamnatin jihar Kano ta dauki wani matakin Shari’ah kan ire-iren wadannan kafafen yada labarai ba.
A kashin gaskiya ma har yanzu ba mu ga Gwamnan da yake zaman lafiya da ‘yan jarida sama da na jihar Kano ba. Duk da cewar wasunsu ba sa yin aikinsu bisa ka’idojin aikin yadda ya tanadar. Har yanzu cikin tsahon kusan shekaru 7 ba wani dan jaridar da Gwamnan ya taba kai wa gaban alkali.
Amma irin wannan cin kashin da a ke ya wa Ganduje me ya sa ba a yi ne a wasu jihohin, musamman ma makotan Kano? An san wargi wuri shi kai. Cin mutunci har da na taba iyalansa ba sau daya ba sau biyu ba ba sau uku ba an sha yi a Jihar ta Kano. Amma ba a taba jin Gandujen Kanawa ya ce uffan ba.
Kuma fa duk da cewar wasu da ba za su iya hakura da wanann cin fuska ga Shugaban su ba, har su ka fara kai karar irin wadanda ke wannan cin zarafi, amma har yanzu, ko da shagube, ba a taba jin Gandujen ya fadi bakaken maganganu kan irin wadannan mutane ba.
Babban abin mamakin ma shine, yadda mutanen da ba su ma san ina daman su da hagunsu suke ba wai sune masu ire iren wadancan ta-ci-barkatan zance. Wallahi a cikin irinsu wadannan mutane wasu idan ka daga su a unguwanninsu, ko Naira Daya ba za a saye su ba.
Kuma wasu ba za su kara fahimtar tsabar hakurin da Ganduje ke da shi ba sai bayan ya sauka daga mulki wani ya hau. Hmmm a nan za ka kara gane wane irin hakuri Allah Ya horewa wannan dattijon.
Sau da yawa fa, shine yake hakurkurtar da mutanensa kan su daure su dinga shanye irin wannan rashin mutunci da a ke masa. Kullum ce musu yake “Ku dinga jurewa ku dinga daurewa da wadannan abubuwan. Wasu ba su san me suke fada ba. Wasu kuma ku yi musu uzurin jahilci da neman abinci.”
Kullum Ganduje ya na nunawa masoyansa da makusantan sa cewar shi fa mai hakuri kullum shi ke da riba. Ai kuwa tabbas ga shi nan ana gani.
Balarabe Yaro Kurna
skabiru863@gmail.com