Daga Umar Usman Sani Mainagge
An gurfanar da Abdulmajid Danbilki kwamanda a gaban kotu majistry Mai lamba 58 karkashin ai sharia Aminu Gabari.
Ana dai zargin Danbilki da laifin Bata suna da kalaman batanci da yunkurin tayar da hankali, yayin wata hira da yayi a Wani gidan Radio, yayi batanci ga gwamnan jihar Kano da zargin baiwa Mai mala buni cin hanci
Sai dai Danbilki kwamanda ya musanta dukkanin laifukan da ake zargin ya aikata Waɗanda Suka hadar da 1. Bata suna
2. furta kalaman kaskanci
3. yunkurin tayar da hankali.
Lauyan gwamnati Barr. Wada A Wada ya shedawa kotu cewa tun da Wanda ake zargi ya musanta zargin Suna rokon wata Rana domin kawo shedunsu a gaban kotun.
Barr wada a wada Yayi rokin da a umarci yansanda su kawo kundin bayansu na bincike akan Wanda ake Kara .
Lauyan Abdulmajid Danbilki kwamanda a gaban kotu Barr. Ibrahim chedi yayi rokon da a Sanya Wanda yake kare a hannun belli kuma zasu tabbatar da cika dukkanin wasu ka’idojin da kotu ta jindaya .
Mai shari’a Aminu Mahd Gabari ya yi umarni ga mai gabatar da Kara da ya kawowa kotu Shedu.
Kuma anyi umarni da a ajiyeshi a gidan gyaran Hali zuwa Ranar 15