Da dumi-dumi:Yan Fashi sun yi yunkurin yin Fashi a gidan Shugaban Ma’aikatan Buhari

Date:

Daga Abubakar Y Na’ Annabi

An yi kokarin yin fashi a gidan Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a cewar fadar shugaban.
 Wani shafin yanar gizo ya ruwaito cewa  Gambari da wani jami’in gudanarwa a fadar shugaban kasa da aka ambata da suna Maikano, an yi musu fashi.


  A cewar rahoton, wanda ke ta yawo a yanar gizo, ‘yan fashi da makami sun mamaye Aso Rock suka kuma kutsa gidajen Gambari da Maikano.


 A wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Kasa ya fitar a Daren litinin din nan ya ce, “Shugaban Ma’aikatan Farfesa Ibrahim Gambari ya tabbatar da cewa akwai” wani yunkuri na wauta “na sata da aka yi  gidansa da karfe 3:00 na safiyar yau amma Yan fashin basu yi nasara ba.


 “Farfesa Gambari, wanda gidansa ke kan titi kusa da Villa ya ba da tabbacin cewa babu wani abin damuwa game da lamarin.”


 Gambari ya gaji marigayi Abba Kyari, wanda ya mutu a wani asibitin Legas yayin da yake jinyar kwayar cutar ta Corona a watan Afrilun shekarar 2020.


 Labarin wani yunkuri na yi wa Gambari fashi ya zo ne a daidai lokacin da fashi da satar mutane suka zama ruwan dare a kasar Nan .


 Gwamnatin Buhari ta kasance cikin matsin lamba sakamakon rashin tsaro a kasar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...