Gobara ta kone Rumbun adana kaya na Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar kano

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Juma’a a rumbun adana kaya na Hukumar bada  agajin gaggawa na jihar Kano (SEMA), Inda ta lalata kadarori na Naira miliyan 18.5 a mariri dake karamar hukumar Kumbotso.
 Sakataren zartarwa na SEMA, Dr Saleh Jili, ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.
 Ya ce lamarin ya afku ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1 na rana a rumbun ajiya na SEMA dake Mariri inda rumbun yake cike makil da kayayyakin agaji da ake baiwa Waɗanda suka hadu da iftila’in gobara da ambaliyar .
 Yace gobarar ta tashi ne sanadiyyar kone yayi da akai a Makarantar first Lady, da ke kusa da rumbun, Inda azuzuwan dalibai uku suka kone kurmus sakamakon kona dajin wanda ya kara tsawaita wutar da ta kone wajen.
 Kayayyakin da gobarar ta lalata sun hada da katifu 450, matashin kai 450, katan 655 na Pampers na manya da yara.
 Sauran kayayyakin da suka kone sun hada da katon din Dettol guda 10, katan 10 na Sinadarin wanke-wanke, kwali 10 na Izal, injin nika, injin dinki, injinan fachi da gidan sauro, da dai sauransu, Waɗanda kudinsu ya kai Naira miliyan 18.5.
 Dr jili kuma yi kira ga jama’a da hukumomin makarantu da su Rika yi taka tsantsan wajen kona daji.
 Jili ya shawarci mazauna garin da su kasance dasu rika kashe kayan wutar lantarki a lokacin da za su fita daga gidajensu ko kuma kafin su kwanta barci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...