A jiya Alhamis ne Jamila Sani, matar Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5 a Jihar Kano, ta bada shaida a kan mijinta.
Tun a zaman kotun na jiha ne lauyan gwamnati, Musa A. Lawal ya gabatar da shaidu guda uku bayan da a zaman kotun na baya Tanko ya nisanta duk tuhume-tuhumen da a ke masa.
Shaidun sun haɗa jami’an ƴan sandan farin kaya, DSS biyu sai kuma ɗan sanda guda daya, wanda shi ne ma wanda ya binciki laifin.
Da a ke mata tambayoyi a zaman kotun na jiya, matar Tanko ta tabbatar da cewa ya kawo Hanifa gidan, inda ba ta fi tsawon kwanaki shida ba.
A cewar matar, da ta tambayi Tanko ko ƴar waye sai ya ce ai ƴar malamar da ke aiki a makarantar sa ne, inda ya ce mahaifiyarta ta samu aiki a Saudi Arebiya shi ne ta tafi Abuja domin cike wasu takardu.
Matar Tanko ɗin ta ƙara da cewa da wasa da wasa sai da Hanifa ta kwana shida a gidan su, sannan da daddare wajen ƙarfe 11 na dare ya ɗauke ta da ga gidan.
Da a ka nuna mata hoton Hanifa, matar Tanko ta tabbatar da cewa ita ce yarinyar da mijin nata ya kawo har ta yi kwanaki 6, har ma ta saba da ƴaƴan ta a gidan.
“Ban san cewa Hanifa ta mutu ba sai da jami’an DSS su ka zo gidan mu, sannan na san halin da a ke ciki,” in ji matar Tanko.
Kadaura24 ta rawaito cewa kawo yanzu dai, an gabatar da shaidu guda takwas a kotun.
Alƙalin kotun, Usman Na-abba, ya umarci a maida waɗanda a ke zargi gidan yari har sai ranar 9 da 10 ga watan Maris za a ci gaba da shari’ar.