Ku fara shirin Hajjin 2022,NAHCON ta fadawa hukumomin alhazai na jihohi

Date:

 

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta umarci hukumomin alhazai na jihohi da su yi maza-maza su fara shirye-shiryen Hajjin 2022.

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, Zikrullah Kunle Hassan, shi ya bada umarnin a Abuja a yayin ganawa da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi a faɗin ƙasar nan.

Wannan matakin na NAHCON ya zo ne bayan da Hukumar ta samu umarnin hakan da ga Saudi Arebiya a kan fara shirye-shiryen Hajjin bana.

Hassan ya yi bayani cewa a bana, Hukumar Hajji da Ummara ta Saudiya ce za ta yi tsare-tsare da shirye-shirye na Hajji, ba kamar shekarun baya ba da hukumomin alhazai na ƙasashen waje ke shiga a yi shirye-shirye na kafin Hajji.

Shugaban NAHCON ɗin ya kuma umarci hukumomin alhazai na jihohi da su mayar da kuɗaɗen da alhazai su ka fara biya zuwa asusun adadin gata na Hajji da ke bankin jaiz domin a daidaita shirin na Hajjin 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...