Daga Aliyu Sufyan Alhassan
Iyaye da masu ruwa da tsaki na da rawar takawa wajen kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi a Kano.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugabar kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya reshen jihar kano wato International Human Right Movement Ambasada Zuhra Abdulhamid Hassan lokacin da ƙungiyar ta kai ziyara ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA anan Kano.
Ambasada Zuhra tace ziyarar da suka kai hukumar tana da alaƙa da haɗa kai don yaƙar shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa.
“Makasudin ziyarar ta mu ita ce domin mu sami hadin kai da Hukumar NDLEA ,sannan mu Hada karfi da karfe don mu yaki matsala shaye-shaye sata fyade da su ka addabi al’ummar kasar nan.” Inji Amb. Zahra
Tace Hukumar ta yi alkawarin zata baiwa Kungiyar hadin kai da goyon baya domin su cimma abun da Kungiyar su ta International Human Right ta Sanya a gaban.
A nasa jawabin babban kwamanda hukumar NDLEA na jihar kano Abubakar Idris Ahmad ya sha alawashin hada kai da kungiyar domin tabbatar da magance shaye shaye a tsakanin matasa.
“Ziyara tana da matukar muhimmanci Kuma mun tattauna da dama Waɗanda Suka jibanci cigaban jihar kano da Kasa baki daya.”inji Amb. Zahra
Yace akwai alaka tsakinin hukumar NDLEA da Kungiyar Saboda Hukumar su saboda Kungiyar tana Kare hakkin al’umma ne mu Kuma muna yaki da Masu Sha da fataucin miyagun kwayoyi, yace nan bada jimawa ba al’umma zasu ga alfanun hadakar mu da Kungiyar.
Daga bisa ya nada shugabar kungiyar kare haƙƙin ɗan adam hajiya Zuhra Abdulhamid Hassan a matsayin jakadiyar yaƙi da wannan dabi’a ta shaye shaye da ta’ammali da miyagun kwayoyi bisa sahalewar shugaban hukumar na ƙasa Gen Buba Marwa.