K/H Kumbotso ta dakatar da aikin titin Sheka Karshen kwalta Saboda Dan Majalisar wakilan yankin yayi mata riga Malam Masallaci

Date:

Daga Jidda Ahmad Diso

 

Karamar Hukumar Kumbotso ta Dakatar da aikin wailari zuwa sheka Bakin kwalta da Dan majalissar tarayya na yankin ya kaddamar Saboda Gwamnatin jiha ta Amincewa karamar Hukuma aikin.

Kadaura24 ta rawaito Cikin Wata wasika da aka aikewa Hakimin Karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Ahmad Ado Bayero wadda Darkatan gudanarwa ta Kumbotso Umma Abbas Sanusi ta Sanyawa hannu a maddadi Shugaban Karamar Hukumar tace ana Sanar da hakimin da sauran masu ruwa da tsaki na yankin cewa Majalisar Karamar Hukumar ta dakatar da Aikin.

Tace dakatar da Aikin Yana da nasa da da yadda Dan Majalisar Kumbotso a Majalisar wakilai ya kawo mashinan aikinti bayan da Gwamnatin Kano ta amincewa Shugaban Karamar Hukumar Hassan Garban kauye farawa gudanar da aikin akan kudi fiye da naira miliyan 500,000,000, Amma daga bisani kafin Fara aikin Dan majalissar yaiwa karamar Hukumar Riga malam mmasallaci ya Fara kaddamar da aikin,hakan tasa Shugaban Karamar Hukamar ya Bukaci Dan majalissar Daya sauyawa Aikin Guri adai wannan mazaba Domin ciyar da yankin gaba.

Sanarwar tace tuni Gwamnatin Jihar Kano ta Amincewa karamar Hukumar ta Gudanar da aikin Wanda kudinsa ya Kai sama da Naira miliyan dari biyar, Rashin Fitar da kudin yasa aka Sami jinkiri wajen Gudanar da aikin titin.

Shugaban Karamar Hukumar Hassan Garban Kauye yayi fatan Dan Majalisar Zai kammala aikin lafiya Kamar yadda aka fara, Inda Kuma ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki da al’umarsu unguwar ta sheka Karshe kwalta dake mazabar wailari zasu baiwa Masu Aikin hadin Kai domin Samun nasarar kammala aikin don cigaban yankin da Karamar Hukumar ta kumabotso baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...