An Kara tabbatar da Muhd Sanusi II Matsayin Khalifan Tijjaniyah na Nigeria

Date:

Daga Abubakar Nurain

Shugaban darikar Tijjaniyya Muhammadul Mahi Niasse ya nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a matsayin halifan Sheik Ibrahim Kaolack kuma shugaban darikar Tijjaniyya a Najeriya a hukumance.


 Mai magana da yawun Mr Sanusi Sa’adatu Baba Ahmad ta sanar da hakan ne a shafinta na Facebook a ranar Litinin.


 Sa’adatu Baba Ahmad ta ce Niasse ya sanar da nadin ne a Madina Baye, Kaolack, Senegal a ranar Lahadi bayan Sallar taraweeh.


 Kadaura24 ta rawaito Tun bayan rasuwar Sheikh Khalifa Isyaku Rabiu a shekarar 2018, kungiyar ba ta nada wani shugaba ba.


 Sarkin Kano Muhammad Sanusi I, marigayi kakan Sabon Khalifan, ya jagoranci Tijjaniyah a Kasar nan.


 Idan za a iya tunawa an nada Sanusi ll a matsayin Khalifa na darikar Tijjaniyya a Najeriya ta hannun Makkiy Niasse kane ga Mahy Niasse, a lokacin bikin Mauludin Sheik Ibrahim Niasse na bana a Sakkwato.

54 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...