Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umurci kwamandojin sojin ƙasar su shirya sojojin Rasha masu kula da makaman nukiliya su kasance cikin shiri.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa a fadar Kremlin wanda ministan tsaro da kwamandan sojojin kasar suka halarta.
Mista Putin ya ce manyan jami’an ƙasashen yammaci sun yi kalamai masu zafi kan Rasha.
Ya kira takunkuman da kasashen yammaci suka ƙaƙabawa kasarsa a matsayin haramtattu.