Shirye-shirye sun yi nisa na sake aurar da zawarawa a Kano – Dr Zahra’u Muhd

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa
 Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta jihar Kano Dr Zahra’u Muhammad ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa na sake Gudanar da auren zawarawa da ‘yan mata a jihar.
Cikin Sanarwar da Jami’ar yada labaran Ma’aikatar Bahijja Malam Kabara ta aikowa Kadaura24 ta ce Malam Zahra’u ta bayyana hakan ne a yayin wani taron daurin aure na mutane 31 maza da mata, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.
Kwamishiniyar ta sake jaddada kudirin gwamnatin kano na shirya irin wannan aure, inda ta bayyana kalubalen tattalin arziki tun daga lokacin COVID-19 a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da suka jinkirta shirin.
 Dr Zahra’u Muhd ta kuma bayyana cewa Insha Allahu shirin zai gudana ne ta hanyar ma’aikatar kula da mata, kuma zata zabi marayu da marasa galihu.
 Daga nan sai ta bukaci ma’aurata da su yi biyayya ga juna, kuma su bi ka’idojin aure Kamar yadda yake a Musulunci.
 Daga nan ta yaba da kokarin Gidauniyar FOMWAN DA DARUL ARQAM da suka shirya taron tare da yin kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...