Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ce kubutar da kimanin mutum 30 cikin 40 da yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke karamar hukumar Jibiya.
An sace mutanen ne lokacin da suke gabatar da sallar Tahajjud.
Kakakin rundunar yan sandan, SP Gambo Isah, ya fada wa BBC cewa lamarin ya faru da tsakar daren ranar Litinin inda yan bindiga da ba a tantance yawansu ba dauke da makamai suka kutsa cikin sabon masallacin da ke Unguwar Kwata.
A cewarsa, “lokacin da suka je sun yi harbe-harbe a sama kuma sun saci masallata wadanda suka fito domin yin sallar Tahajjud.”
Ya ce bayan sun samu rahoton ne jami’an tsaro da yan kato-da-gora da kuma al’ummar gari suka yi gangami inda suka bi yan bindigar abin da ya ba su damar kubutar da mutum 30 cikin wadanda aka sace.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan ya kara da cewa binciken da suka yi bayan kubutar da mutanen ya nuna cewa akwai sauran mutum 10 da ba a san inda suke ba.
Ya ce ba za su iya tantancewa ko ragowar mutanen na hannun yan bindigar ne ko kuma sun tsere ba.
SP Gambo Isah ya ce tuni mutanen da aka kubutar suka koma hannun iyalansu – babu wani da aka harba ko ya samu rauni.
“Babu wani a iya saninmu da aka kai asibiti saboda ya ji rauni,” in ji SP Gambo Isah.
A cewarsa, jami’an yan sanda sun bi sawun yan bindigar kuma an gano cewa sun bi ta Tsambe kuma sun nufi Dumburun da ke jihar Zamfara.
Sai dai wasu al’ummar yankin sun fada wa BBC cewa mutanen da kansu suka tsira ba wai yan sanda bane suka kubutar da su.
Ko a baya-bayan nan ma sai da yan bindiga suka sace daliban Kankara inda masu fafutuka sun sha sukar Shugaba Muhammadu Buhari wanda ɗan jihar Katsina ne da rashin tabuka abin a zo a gani na murkushe yan bindiga.
Najeriya dai na ci gaba da fuskantar karuwar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na kasar.
Jama’a na neman gwamnati ta dauki matakan magance matsalolin duk da a lokuta da dama gwamnatin na ikirarin tana duk mai yiwuwa na kawo karshen matsalolin