Dakarun Sojin Kasar nan sun hallaka ‘yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara

Date:

Daga Saifullahi Ahmad Gwammaja 

 A daren Lahadi ne rundunar sojin Najeriya tace dakarun runduna ta 8 da aka tura yakar ‘yan bindiga da suka addabi Zamfara da jihohi dake da makwabtaka dasu sun kashe kwamandojin ‘yan bindiga 5 tare da wasu miyagu 48 bayan musayar wuta da aka yi. 


Har ila yau, dakarun sun yi kokarin ceto mutum 18 da aka yi garkuwa dasu daga sansanin ‘yan bindigan, Kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito. 


Birgediya janar Mohammed Yerima, daraktan hulda da jama’a na sojin kasa, wanda ya sanar da hakan a wata takarda ya kara da cewa an tarwatsa sansanin ‘yan bindiga masu yawa inda aka samo miyagun makamai. 


Ya ce, “Dakarun runduna ta 8 ta sojin kasa dake aiki a Zamfara da sauran jihohi sun samu manyan nasarori a yaki da ‘yan bindiga da suke yi. 


“Rundunar tun farko ta kaddamar da sabon atisaye mai suna Operation Tsare Mutane bayan umarnin da suka samu daga shugaban sojin kasa, Laftanal Kanal Ibrahim Attahiru. 


“Babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Usman Yusuf ya kaddamar da atisayen wanda zai fara daga 23 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afirilun 2021 a karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara. 


“Cike da nasara dakarun suka tarwatsa sansanonin ‘yan bindigan dake Jaya, Kadaya da Bayan ruwa da sauransu. 


 “Dakarun sun yi nasarar sheke ‘yan bindiga 48 yayin da shugaban ‘yan bindigan yankin, Jummo ya samu miyagun raunika a kafafunsa. Dakarun sun ceci mutum 18 da ‘yan bindigan suke rike dasu.


 “An samo bindigogi kirar AK47 8 da wasu miyagun bindigogi hudu daga ‘yan bindgan. “Kwamandojin ‘yan bindigan 5 da suka hada da Yellow Mai-Bille, Sani Meli, Dan- Katsina da Sama’ila Bakajin Bari duk sun sheka lahira yayin da Nasanda ya sha da kyar.” 

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...