A daidai lokacin da dakarun Rasha ke ƙara matsawa cikin babban birnin Ukraine wato Kyiv, hukumomin Ukraine ɗin na kira ga ƴan ƙasar da su yi duk mai yiwuwa domin kare ƙasarsu daga kutsen Rasha.
Mai bayar da shawara a ma’aikatar harkokin cikin gida na ma’aikatar tsaro ta Ukraine Vadym Denysenko, ya ce tuni aka bayar da bindigogi masu sarrafa kansu 18,000 ga ƴan sa kai waɗanda ke son kare babban birnin ƙasar.
BBC Hausa ta rawaitoMa’aikatar tsaro ta ƙasar da ma’aikatar harkokin cikin gida duk sun roƙi jama’ar ƙasar da su ankarar da hukumomin ƙasar idan suka ga gittawar dakarun Rasha haka kuma a kai musu hari da bam ɗin fetur na kwalba.