Baya ta haihu, ba a daura auren Aisha Tsamiya ba a yau ko, me ya faru ?

Date:

Daga Khadija Abdullahi Umar

 

BAYA ta haihu. Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ba a yau Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 ne za a ɗaura mata aure kamar yadda aka yaɗa a soshiyal midiya.

Wannan sabuwar sanarwar ta biyo bayan yaɗa wani katin gayyatar aure ne wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ana cewa na auren jarumar ne.

A katin, an nuna cewa fitacciyar jarumar za ta yi aure a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022.

A katin, wanda Kadaura24 ta gani, an bayyana sunan sahibin nata, wato Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano.

Tun da labarin auren ya ɓulla a soshiyal midiya abokan sana’ar A’isha su ka shiga yi mata fatan alheri, inda kusan dukkan su sun ɗora hoton ta tare da katin auren.

To amma a daren jiya  Aisha Tsamiya ta hau Instagram ta rubuta cewa, “Assalamu alaikum, jama’a barkan mu da warhaka. Na gode da addu’o’in ku da fatan alkhairi, na ji daɗi sosai, amma aure na ba 25th ga wannan watan ba ne, sai next month in-sha Allah……Na gode Allah ya saka da alkhairi.”

Wannan sanarwar, wadda Tsamiya ta yi a shafin ta na Instagram mai mabiya sama da miliyan ɗaya, ta baiwa mutane da dama mamaki.

A’isha Tsamiya dai ta na ɗaya daga cikin jaruman Kannywood da wasu ke ganin kamar sun ƙi aure ne.

Wasu kuma su na yi mata kallon mayaudariya, don su na cewa akwai lokacin da ta yaudari darakta Mu’azzam Idi Yari da kuma jarumi kuma mai bada kayan sawa (costumier) Sadiqu Atis.

Jaridar fim Magazine Haka kuma a ‘yan shekarun baya har an gama maganar auren ta da wani attajiri da ke Jihar Kebbi, wanda aka sa bayan ta dawo daga aikin Hajji za a yi bikin, ta na dawowa sai kuma labari ya canza, aka fasa auren. Wasu na cewa ita ce ta ce ta fasa auren, yayin da wasu su ka riƙa cewa shi ne ya fasa saboda wasu dalilai.

Kafin wannan lokaci, an ɗauki tsawon lokaci ba a jin ɗuriyar jarumar a Kannywood, musamman a yanzu da masana’antar ta koma cin kasuwa a YouTube.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...