Ba da jimawa ba Shugaban Ukraine Volodymyr Zelesnky ya yi jawabi ga ƙasarsa. Ga bitar wasu daga cikin abubuwan da ya fada.
- Zelensky ya bayyana cewa aƙalla mutanen ƙasarsa 137 aka kashe a yaƙin nan zuwa yanzu, ciki har da farar hula. Haka kuma akwai mutum 316 da aka raunata.
- Shugaban Ukraine din na ganin shi ne mutum na farko da Rasha ke hari. Ya ce ba shi da niyyar barin gidan gwamnatin da yake zaune a birnin Kyiv.
- Ya kuma tabbatar da rahotannin da ke cewa Rasha ta harba makamai masu linzami masu yawa a cikin Ukraine da misalin ƙarfe huɗu na asuba agogon ƙasar.
- Ya kuma ƙara kira ga ƙasashen yamma da su ƙara ƙoƙari kan saka takunkumai ga Rasha inda ya buƙaci su yi abin da ya fi saka takunkumin tattalin arziki ga Rasha.
- A wani gargaɗi da ya yi ga Moscow, Zelensky ya bayyana cewa Ukraine ba za ta daina kare kanta ba har sai Rasha ta daina abin da take yi.